Romans 9

1Gaskiya ne nake gaskiya nake fada cikin Almasihu. Ba karya nake yi ba. Lamirina, na shaida a cikin Ruhu Mai Tsarki. 2cewa ina da matukar bakin-ciki da takaici marar karewa a zuciyata.

3Dama ace, a la’anta ni, in rabu da Almasihu saboda ‘yan’uwana, wato dangina da suke zuriyata bisa ga jiki. 4Sune Isra’ilawa, sun sami karbuwa, da daukaka, da baiwar shari’a, da yi wa Allah sujada, da alkawarai. 5Dukkan ubanni nasu ne daga cikinsu Almasihu ya fito bisa ga jiki- wanda shi ke Allah bisa kowa. Yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin.

6Amma ba wai alkawarin Allah ya kasa ba ne, ba dukkan Isra’ilawa ne suke Isra’ilawa na gaskiya ba. 7Haka nan, ba dukkan zuriyar Ibrahim ne ‘ya’yansa ba. Amma ‘’ta wurin Ishiyaku ne za’a kira zuriyarka.‘’

8Yana nuna mana cewa ba ‘ya’yan jiki su ne ‘ya’yan Allah ba. Amma ‘ya’yan alkawari ne ake kirga su, kuma aka kebe su. 9Wanna ce kalmar alkawari, ‘’badi warhaka zan dawo, Saratu kuwa zata sami da.‘’

10Amma ba wannan kadai ba, bayan Rifkatu ta dauki ciki daga gun mijinta, ubammu Ishiyaku. 11Yaran nan kafin ma a haife su, balle ma a ce sun yi wani abu mai kyau ko laifi, saboda zaben da Allah yayi, bai danganta da abin da suka yi ba, ko don aiki ba, amma don shine mai kira-- 12kamar yadda Ya ce, mata, “babban zaya yiwa karamin bauta,‘’ haka nassi yace, 13‘’Kamar yadda aka rubuta: “Yakubu na ke kauna, amma Isuwa na ki shi.”

14To me zamu ce kenan? Allah ya yi rashin adalci kenan? Ko kadan. 15Gama ya ce wa Musa, ‘’Ina nuna jinkai ga wanda zan yi wa jinkai, zan ji tausayi ga wanda zan tausaya masa.‘’ 16Saboda haka, ba don wanda ke da aniya ba ne, ko kuwa wanda yake kokari ba, amma saboda Allah mai nuna jinkai.

17Gama nassi ya ce da Fir’auna, ‘’ Saboda wannan dalilin ne, na tada kai, don in nuna ikona mai karfi a kanka, don sunana ya yadu ga dukkan duniya.‘’ 18Ta haka Allah ya nuna jinkansa ga wanda ya so, ya taurarar da zuciyar wanda ya ga dama.

19Za kuce mani, to don me, ‘’Yake kama mu da llaifi? Wa ya taba yin jayayya da nufinsa?‘’ 20In ma mun duba, kai mutum wanene kai da zaka ja da Allah? Ko abin da aka gina zai ce wa magininsa, ‘’Don me yasa ka ginani haka?‘’ 21Ko maginin ba shi da iko akan yimbu daya da zai gina tukunya mai daraja, wata kuma tukunyar don kowanne irin aiki?

22In ace Allah, dake niyyar nuna fushinsa da ikonsa, ya sanu, sai ya jure da matukar hakuri mai yawa da tukwanen fushi da ya shirya don hallakarwar fa? 23To ko ma ya yi haka don ya nuna yalwar daukakarsa da take dauke da alheri, wanda ya shirya don daukakarsa tun farko? 24Zai yiwu ma ya yi haka ne domin mu, mu da ya kira, ba ma daga cikin Yahudawa kadai ba, amma har ma daga cikin al’ummai?

25Kamar yadda ya ce a cikin littafin Yusha’u: ‘’zan kira wadanda ba mutanena ba mutanena, da kuma kaunatattunta wadanda ba kaunatattu ba. 26Zai zama kuma a inda aka ce da su, “ku ba mutanena bane, za a kisa su ‘ya’yan Allah mai rai.”’

27Ishaya ya yi kira game da Isra’ila, ‘’in a ce yawan ‘ya’yan Isra’ila zasu zama kamar yashi a bakin teku, ragowarsu ne kawai za su sami ceto. 28Ubangiji zai tabbatar da cikar kalmarsa a duniya, ba kuwa da dadewa ba. 29Yadda Ishaya ya rubuta ada, ‘’In da ba Ubangiji mai runduna bai bar mana zuriya ba, da zamu zama kamar Saduma, da kuma an maida mu kamar Gomarata.

30To me za mu ce kenan? Ko al’ummai, da ba sa neman adalci, sun samu adalci ta wurin bangaskiya. 31Amma Isra’ila, wadanda suka nemi adalcinsu ta wurin shari’a, ba su kai ga gaci ba.

32To don me? don ba su neme shi da bangaskiya ba, amma ta ayyuka. Sun yi tuntube a kan dutse da zai sa laifi. Kamar yadda aka rubuta, “Ga, shi na ajiye dutse a kan Sihiyona dutsen tuntube mai sa laifi. Ga wanda ya bada gaskiya gare shi ba zai ji kunya ba.”

33

Copyright information for HauULB